Sarkin Musulmi ya bada umarnin fara duban jinjirin watan Babbar Sallah

Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta (NSCIA) kuma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bukaci al’ummar Musulmin da su sanya ido kan ganin jinjirin watan Zul-Hijja na 1445AH bayan faduwar rana a yau Alhamis 29 ga watan Zul-Qa’dah 1445AH, daidai da ranar Alhamis 6 ga watan Yuni 2024.

Sultan Abubakar III ya bada umarnin ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin babban sakataren hukumar, Farfesa Salisu Shehu a jiya Laraba.

Watan Zul-Hijja, wata na 12 kuma na karshe a cikin kalandar Musulunci, yana daya daga cikin watanni hudu masu alfarma a Musulunci da musulmin duniya ke gudanar da aikin hajji da bukukuwan Sallah Eid-El-Kabir.

A cikin wannan wata ne alhazan musulmi daga sassa daban-daban na duniya ke taruwa a birnin Makkah na kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin da za a fara a ranar takwas ga wata, da kuma gudanar da bukukuwan Sallah daga ranar 10 zuwa 13 ga watan Zul Hijjah.

Comments (0)
Add Comment