Sanata Bala Mohammed ya bayyana karramashi da aka yi a matsayin babbar nasara

Gwamnan jihar Bauchi a arewacin Kasarnan Sanata Bala Mohammed ya shaida wa manema labarai cewa lambar yabon da wata gidauniya da hadin gwiwar gwamnatin Najeriya suka karramashi da ita, babbar nasara ce.

Sanata Bala ya ce an ba shi lambar yabo ta ayyukan birane, sakamakon irin ayyukan da gwamnatinsa ke yi a jihar ta Bauchi, ya kuma ce a yanzu zai mayar da hankali kan kara inganta tsaro a jiharsa.

Sanata Bala ya kuma tabo batun bai wa malamai da sarakunan jiharsa girma da kimarsu: ”Za a gyara albashin sarakuna da limamai ta yadda su ma za su kula da na su iyalan.”

A baya dai lokacin da aka yi taro na gwamnonin arewacin Najeriya, gwamnonin yankin sun yi korafin cewa an mayar da yankinsu saniyar-ware, kuma Sanata Bala ya kara jaddada cewa yankin arewa maso gabas na cikin wani yanayi da koma-baya ta kowanne fanni.

Wasu dai na mamakin yadda mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya fito daga arewa maso gabashin kasar, amma kuma yankin na koma-baya.

A kan haka gwamnan ya ce ba lallai mataimakin shugaban kasa ya iya wannan yakin inganta yankin arewacin kasar shi kadai ba, watakil ma wani ministan gwamnati zai fi shi samun dama.

Kan batun bai wa kananan hukumomi cin gashin kansu da harkokin kudu da shugabanci da ake ganin gwamnoni kamar ba sa son hakan, gwamnan Bauchin ya ce gwamnatin tarayya ke musu barazana.

Ya ce a yadda ake tafiya suna bakin kokarinsu, kuma kundin tsarin mulkin Najeriya ya kawo hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihohi da kananan hukumomi wato ta hanyar asusun hadin gwiwa.

A karshe Sanata Bala ya yi kira ga gwamnatin tarayya, da cewa: ”A gaskiya ya kamata a ji tausayinmu, a tuna muna da dimbin al’umam.”

Comments (0)
Add Comment