Tsohon shugaban majalisar dattawa mai wakiltar Yobe ta Arewa, Ahmad Lawan, ya nemi a binciki rikicin da ya barke tsakanin sojoji da fararen hula, wanda ya yi sanadin kashe fararen hula uku a Gashu’a, dake karamar hukumar Bade a jihar Yobe. . Rahotanni sun ce sojojin sun yi ta harbi ba kakkautawa cikin gungun masu zanga-zangar da ke tunkarar shingen bincikensu da ke kusa da gadar Gashua don nuna adawa da kisan wani ma’aikacin babur mai kafa uku. Shugaban majalisar dattawan ta tara, a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi, ya bukaci rundunar sojin kasar nan da ta gaggauta gudanar da bincike kan lamarin. Ya kuma yi kira ga jama’ar yankin da su kwantar da hankalinsu, yayin da ya tabbatar da cewa tuni ya tattauna da hukumomin soji domin ganin an kama wadanda suka aikata laifin tare da hukunta su kamar yadda doka ta tanada.