Sanata mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso Gabas,Brr. Ibrahim Hassan Hadejia ya bada gudunmawar takunkumin rufe hanci da baki guda dubu goma da dari shida da talatin ga makarantu domin rabawa daliban mazabarsa.
Wakilin Sanatan, Muhammad Lawan wanda ya mika gudunmawar kayayyakin yace hakan zai taimaka wajen marawa kudirin gwamnati baya na yaki da yaduwar cutar corona.
- Tinubu ya tsammaci sakayyar alheri daga ‘yan Jigawa a zaben 2027 – Gwamna Namadi
- Gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da N548M ga kungiyar malamai ta Najeriya
- Ba lallai Najeriya ta cike kujerun aikin Hajjin bana da aka ware mata ba
- An sace wasu mata biyu malaman coci a jihar Anambra
- Gwamnatin jihar Jigawa na ci gaba da biyan hakkokin wadanda sukayi ritaya
Ya kuma bukaci malamai da dalibai dasu yi cikakken amfani da shi wajen kare kai daga kamuwa daga cutar inda kuma ya yabawa ma’aikatar ilmi bisa tsare-tsaren da tayi na samun nasarar rubuta jarabawar karshen ga dalibai.
Kazalika, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia ya bada gudunmawar kayayyakin bada horo ga cibiyar rubuta jarabawar kammala sakandare ta NECO dake makarantar sakandaren Famfo Goma.