A jiya Asabar ne Shugaba Muhammadu Buhari ya koma babban birnin tarayya Abuja bayan ziyarar aiki ta kwana tara, wadda ta haɗa da yin bikin Sallar layya tare da ‘yan uwansa da kuma ƙaddamar da wasu ayyuka a Jihar Katsina.
Kafin Komawarsa Muhammadu Buhari ya hori sojojin dake yaƙi don kakkaɓe ya bindiga daɗi da su yi aiki tuƙuru wajen dawo da zaman lafiya a ƙasar nan, musamman a jihohin da mahara suka addaba.
Ya bada umarnin ne lokacin da ya yi wa sojoji jami’ai 15, da sojoji 160 na 17th Army Brigade da Nigerian Air Force 213 Operational Base a Katsina ƙarƙashin “Operation Hadarin Daji” a Filin Jirgin Saman a Katsina.
Yayinda yake mahaifarsa, Daura, Shugaba Buhari ya karɓi baƙuncin Shugaban Guinea Conakry, Farfesa Alpha Conde, inda shugabannin ƙasashen biyu suka yi Sallar Idi a Daura ranar Lahadi.
A yayin zamansa a Daura, Shugaban Ƙasar ya karɓi baƙuncin mambobin Ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC da shugabancin Majalisar Dokoki ta Ƙasa dana Majalisar Dokokin Jihar Katsina waɗanda suka kai masa ziyarar Salla.