Sai An Rage Ma’aikata Kafin A Fara Biyan Mafi Ƙarancin Albashi- Ngige

A jiya Alhamis ne Ministan Ƙwadago Da Samar Da Aikin Yi, Dakta Chris Ngige, ya ce buƙatar Ƙungiyar Ƙwadago na neman sabon mafi ƙarancin albashi zai sa Gwamnatin Tarayyar ta kashe kimanin Biliyan ₦580 duk shekara.

Mista Ngige ya ce wannan gyaran albashi, da yake tare da buƙatar ma’aikata, ba abu ne da zai yiwu ba, kuma dole gwamnati ta sallami wasu ma’aikata don ta samu ta iya biyan sabon mafi ƙarancin albashin.

Ministan ya ce gwamnati ba za ta iya biyan waɗannan kuɗaɗe ba yanzu, yana mai ƙarawa da cewa inda Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da hankali shi ne kan ma’aikatan dake kan darajar albashi ta 1, mataki na 1, da darajar albashi ta 6, mataki na 1, inda ma’aikatan za su ji ƙarin albashi sosai.

Ministan ya bayyana haka ne ranar Alhamis a Abuja lokacin da Shugabancin Haɗaɗdiyar Ƙungiyar Ƙwadago, ULC, ƙarƙashin jagorancin Shugabanta, Joe Ajaero ya kai masa ziyarar ban-girma.

Yayinda yake kira ga ma’aikata da su nuna fahimta don taimaka wa halin da Gwamnatin Tarayya ke ciki, Mista Ngige ya ce halin tattalin arziƙi da a ke ciki zai iya hana sabuwar dokar aiki.

Ya ce gwamnati tana ƙoƙarin kauce wa yanayin da zai sa ta sallami ma’aikata, yana mai ƙarawa da cewa wannan zai ƙara wa ‘yan ƙasa wahala.

Mista Ngige ya yi kira ga Ƙungiyar Ƙwadagon da ta yi karɓi tayin ƙarin albashi daga matakai na 7 zuwa 17, yana mai ƙarawa da cewa wata uku ne kawai suka rage wa Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da dokar sabon mafi ƙarancin albashin.

Ya ce gwamnati ba za ta faɗa wa Ƙungiyar Ƙwadago abinda ba za ta iya biya ba, yana mai cewa ba ma’aikacin da ya kamata a ce yana bin gwamnati bashin albashi.

Ministan ya ce: “Babu wata matsala don an samu rashin jituwa a tsarin ƙwadago, za mu iya samun rashin jituwa wani lokaci, daga baya kuma mu cimma matsaya a kan mafi ƙarancin albashin na ƙasa, hakan yana nufin ƙarin Biliyan ₦580 idan gwamnati ta amince da abinda ‘yan ƙwadagon ke buƙata.

“Gwamnati ba za ta iya biyan irin wannan kuɗi ba, duk da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fi sha’awar kyautata wa ƙananan ma’aikata, waɗanda su ne ke kan darajar albashi ta 1 mataki na 1da darajar albashi ta 6 mataki na 1, waɗannan su ne waɗanda ₦30,000 za ta yi wa amfani sosai.

“Gwamnati ta yi nata ɓangaren, kuma sun kawo abinda za su iya amfani da shi don kare wadannan sabon ƙarin albashi. Matakan albashi na 1 zuwa 6 ba su da matsala, amma 7 zuwa 14, da 15 zuwa 17, wannan shi ne inda muke da matsala.

“Da zarar ka gama da mafi ƙarancin albashi, sannan ka tafi wajen aiwatarwa, kana ƙoƙarin cimma wata matsaya da kowa zai amince da ita, da zarar ka fara ƙoƙarin cimma matsaya, sannan sai batun iya biya ta zo.

“To, idan ka tilasta gwamnati ta je ta amince da ƙarin albashi wanda ƙarfinta ba zai iya ɗauka ba, to fa a kaikaice kana umartar ta ne ta rage ma’aikata, don ‘yan kaɗan ɗin da za su rage su samu waɗannan manyan kuɗaɗe.

“Ba ma son haka, daga 2015, Shugaban Ƙasa ya fito fili ya ce ba ya so ya ƙuntata wa ‘yan Najeriya kuma ba ya so ya haifar da rashin aikin yi, kuma duk da haka, yawan al’ummarmu yana ƙaruwa, kuma arziƙimmu ba ƙaruwa yake yi ba balle mu iya ɗaukar nauyin kowa, shi yasa muke da matasa da yawa marasa aikin yi suna gararamba a tituna.

“Muna buƙatar mu cimma wata yarjejeniya nan ba da daɗewa ba, don mu yi amfani da kasafin kuɗin 2019 don mu gyara wannan ƙarin albashin saboda ba zai yi kyau ba a ce idan muka kasa aiwatar da haka, kuma muka gama wannan shekarar kuɗin a Disamba, saboda tsarin kasafin kuɗi zai dawo Janairu zuwa Disamba daga 2020, to wata uku ne kawai suka rage mana.

Ya nuna rashin jin daɗi bisa gazawar tawagar sasantawa ta gwamnati da ta ‘yan ƙwadago na cimma matsaya a kan ƙarin albashin, yana mai jaddada cewa ma’aikatan dake matakan 7 zuwa 14 da 15 zuwa 17 suna da ƙarfi.

Tuni dai Ƙungiyar Ƙwadago ta fara sanar da mambobinta da su tsunduma yajin aiki daga ranar 16 ga Oktoba.

Mista Ajaero, a jawabinsa, ya yi kira ga ministan da ya fara aiwatar da biyan sabon mafi ƙarancin albashin, yana mai jaddada cewa dole su ma kamfanoni masu zaman kansu su biya ₦30,000.

Ya ce akwai buƙatar a gyara tsofaffin dokoki waɗanda ba su yi dai-dai da zamani ba, yana cewa wani yanayi da kamfanoni masu zaman kansu ke biyan ma’aikatansu ₦10,000 zuwa ₦15,000 ba za a amince da shi ba.

KudiMaaikata
Comments (0)
Add Comment