Saboda Batanci Ga Annabi, An Rufe Kafafen Sada Zumunta A Pakistan

Hukumomi sun rufe kafafen sada zumunta a ranar Juma’a a Pakistan, inda a halin yanzu Facebook, Twitter, Instagram, WhatsApp da TikTok ba sa aiki, har da Islamabad, babban birninta.

Gwamantin Pakistan ta yi hakan ne saboda tsoron masu tsattsauran ra’ayin Islama na iya amfani da su wurin tayar da tarzoma a kan hotunan batancin da aka yi wa Annabi Muhammad (SAW) a Faransa a bara.

“An rufe kakafen sada zumunta na was sa’o’i saobda masu neman haddasa rikici ba za su yi amfani da su ba lokacin Sallar Juma’a,” inji wani jami’in gwamnati.

Magoya bayan kungiyar TLP, mai goyon bayan dokar batanci ta Pakistan sun yi dandazo tare da rufe hanyoyi a yayin da suke gudanar da zanga-zangar da suka faro ranar Litinin.

Masu zanga-zangar na bukatar Gwamnatin Pakistan ta cika alkawarin da yi na korar Jakadan Faransa a kasar, kafin ranar 20 ga watnan Afrilu, 2021.

Zanga-zangar ta ritsa da rayukan mutum biyar, ciki har da jami’an ’yan sanda biyu, lamarin da ya sa Ofishin Jakandancin Faransa da ke Islamad umartar Farasawa su fice daga Pakistan na wani lokaci.

Jam’iyyun siyasa da kungiyoyin da ‘yan tayar da kayar baya, ciki har da reshen Kungiyar Taliban a kasar na yawan amfani da kafafen sada zumunta domin ganawa da mabiyansu.

https://aminiya.dailytrust.com/an-rufe-kafafen-sada-zumunta-a-pakistan

Comments (0)
Add Comment