Ruwan sama yayi sanadiyyar mutuwar mutum hudu da batan mutum biyu a jihar Yobe

Ruwan sama yayi sanadiyyar mutuwar mutum hudu da batan mutum biyu a jihar Yobe

Mutane biyar sun mutu yayin da wasu biyu suka bace sakamakon ruwan sama da aka yi a garin Potiskum na jihar Yobe.

Yankunan da abin ya shafa a cewar wani mazaunin yankin, Adamu Yunusa sun hada da Tandari da Yindiski da Dadin Kowa da Gadan Talaka da kuma gundumar Jigawa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Sakataren zartarwa na Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe, Dr Mohammed Goje ya ce an tura tawagar bincike da ceto zuwa yankin domin tantance yawan barnar da ambaliyar ta haifar.

Wata mazauniyar garin, Falmata Ali, wacce ‘ya’yanta biyu suka mutu a lamarin yayin bacci, ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su samar da mafita ta dindindin ga ambaliyar da ake samu kowace shekara.

Comments (0)
Add Comment