Wani ruwan sama mai karfin gaske yayi awon gaba da gidaje da gonaki masu dunbin yawa a jihar kaduna.
Ambaliyyar ruwan ta afkune sanadiyyar wani ruwan sama mai karfi da aka fara shi tin daga daren litinin har zuwa washegarin ranar talata.
Sanadiyyar wannan mamakon ruwan saman ne yasa mutane da dama suka tserewa muhallansu a jihar ta kaduna.
Wannan ambaliyyar ta zo ne makonni kadan bayan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar kaduna, ta fitar da rahoton cewa wasu kananan hukumomi a jihar ka iya fuskantar ambaliyyar ruwa.
Inda hukumar tayi kira da mazauna wajan da abin zai iya afkuwa da su kauracewa gidajensu, amma mazauna garuruwan suka ki bin shawarar hukumar.
Wuraren da ambaliyyar ta shafa sun hada da hanyar Abubakar Kigo, Barnawa, Kudenda, Ungwar Dosa, da dai sauransu.
A cewar wani jami’in hukumar, ambaliyyar ta faru ne sanadiyyar cushe magudanar ruwa da wasu mazauna unguwanni keyi da zuba shara a kwalbati.