Hukumar agajin gaggawa ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane 6 da rushewar gidaje 600 da wata guguwa mai karfi ta jawo a yankunan kananan hukumomi 4 na jihar.
Babban sakataren hukumar, Sale Jiji, ya tabbatar da aukuwar iftila’in ga manema labarai a Kano, inda ya kara da cewa kimanin mutane dubu 1 da 752 ne suka rasa muhallansu sanadiyyar guguwa cikin mako guda da ya gabata.
Ya lissafa kananan hukumomin da lamarin ya shafa da suka hada da Gwale, da Rimin Gado, da Gwarzo da kuma Kibiya.
Yace wadanda suka rasa muhallansu, na samun mafaka a gidajen yan’uwansu a kauyukan da abin ya shafa.
Sale Jiji ya sanar da cewa wutar lantarki ta kashe wani mutum guda a unguwar Ja’en, yayin da wasu mutane 5 suka mutu bayan gini ya rubza musu a yankin karamar hukumar Gwale.