Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a jiya ta ce an kama wasu mutane 61 da ake zargi da aikata laifukan bangar siyasa a kokarinta na kawar da duk wani nau’in laifukan zabe musamman a lokutan yakin neman zabe..
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mamman Dauda ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna-Kiyawa, ya raba wa manema labarai a Kano..
A cewar sanarwar, an yi kamen ne bisa umarnin babban sufeton ‘yan sanda na kasa, Usman Alkali-Baba, na tabbatar da an gudanar da zaben cikin lumana tare da magance matsalar ‘yan bangar siyasa.
A wani labarin daga Kano, Hukumar Kula da Hakowa da Cinikin Man Fetur ta Kasa ta rufe gidajen mai guda 14 domin sayar da mai sama da farashin da gwamnati ta amince da shi a Kano.
Kodinetan hukumar a jihar, Aliyu Muhammad-Sama ya bayyana haka a yayin wani atisayen sa ido da zagaye jiya a Kano.
Ya ce hukumar ta rufe gidajen man bisa sayar da man a kan naira 295 da kuma naira 300 kowace lita sama da farashin da aka kayyade.