Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane 14 a wani hadarin mota a karamar hukumar Ringim

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 14 a wani hadarin mota a karamar hukumar Ringim.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, ASP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da faruwar lamarin a yau a Dutse.

Shiisu Adam ya ce hadarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 7 da minti 40 na yamma, a kan hanyar Ringim zuwa Kano.

Ya ce wasu mutane takwas sun jikkata a hadarin da ya faru a kusa da Kwanar Gerawa a karamar hukumar.

Ya bayyana matan da suka mutu da suka hada da Zainab Hamza da Hauwa Hamza da Gadatu Adamu da Bilkisu Harisu da Ilham Kamilu da Bilkisu Kamilu da kuma Hajjo Yusuf.

Kakakin yansanda ya bayyana mazan da suka rasu, wadanda suka hada da Usman Isiyaku da Nura Umar da Abdullahi Yahaya da Adamu Ahmad da Abdullahi Garba da kuma Yawale Salihu.

A cewarsa, fasinjojin 8 da suka jikkata a halin yanzu suna karbar magani a babban asibitin Ringim.

Comments (0)
Add Comment