Rundunar Sojojin Saman Najeriya ta yi nasarar kashe ƴan ta’adda masu yawan gaske

Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya wato (NAF) ta ƙaddamar da hare-haren sama da suka yi nasara kan maɓoyar ƴan ta’adda a jihohin Kaduna da Zamfara, inda ta kashe ƴan ta’adda masu yawan gaske.

An kai harin ne a ranar 21 ga Agusta, 2024, bayan samun wasu bayanan sirri da suka gano a dajin Mallum a Jihar Kaduna a matsayin sansanin ‘yan ta’adda da ke da alhakin hare-haren baya-bayan nan a ƙaramar hukumar Shiroro a Jihar Neja.

A cewar mai magana da yawun NAF, AVM Edward Gabkwet, ƴan ta’addan sun koma dajin Mallum bayan sun tsere daga dajin Alawa a Jihar Neja.

An kai hari da jirgin sama kan sansanin ƴan ta’addan, inda majiyoyi daga yankin suka tabbatar da mutuwar ƴan ta’adda da dama.

Haka zalika, a wani harin makamancin wannan da aka kai a ƙaramar hukumar Maradun a Jihar Zamfara, an samu nasarar hallaka ƴan ta’adda a maboyar su da ke Bayan Ruwa, inda aka bibiyi su har zuwa inda suka buya.

Comments (0)
Add Comment