Rundunar sojin sama ta Operation Hadarin Daji ta kai samame maboyar ‘yan ta’addan Ado Aliero da Dankarami a jihohin Zamfara da Katsina.
An gudanar da aiyukan ta sama a kananan hukumomin Zurmi, Tsafe, Faskari, da Jibia dake jihohin Zamfara da Katsina tsakanin ranakun 28 zuwa 29 ga watan Yuli.
An tattaro cewa an kashe ‘yan ta’adda akalla 16 a farmakin da jiragen yakin suka kai a yankunan Dankarami.
Wani rahoto da rundunar soji ta fitar kan ayyukan da wakilinmu ya gani a ranar jiya Talata ya bayyana cewa, an gudanar da samamen ne bayan samun rahoton sirri.
Da aka tuntubi kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet, ya bayyana cewa, babban hafsan hafsan sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar, ya bayar da umarnin a kara kai hare-hare a yankin.