Rundunar soji sun kaddamar da wani sabon tsarin yaki da masu satar mai a yankin Neja Delta

Rundunar sojin kasar nan tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan Najeriya da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) da sauran jami’an tsaro a jiya sun kaddamar da wani sabon yaki a kan masu satar mai a yankin Neja Delta domin inganta hako mai tare da farfado da martabar al’ummar kasar.

Sabon yaki da satar mai a yankin Neja Delta ya biyo bayan wani sabon umarnin da shugaban kasa ya bayar ga sojoji da kamfanin NNPC da sauran hukumomin tsaro na inganta hako danyen mai a yankin.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan wata ganawar sirri da shugabannin NNPC da shugabannin hukumomin tsaro, babban hafsan hafsoshin tsaron, Janar Christopher Musa ya ce shugaban kasar ya ba su wa’adin tabbatar da cewa sun tabbatar da tsaron yankin Kudu-maso-Kudu baki daya. 

Kamfanin NNPC da sauran su don gudanar da ayyukansu na inganta hako mai.

Ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za su ga sakamakon sake zafafa yaki da satar man fetur cikin watanni uku. 

Comments (0)
Add Comment