Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta ce ta yi nasarar dakile yunkurin aikata fashi da makami tare da kwato alburusai a dajin Shafar dake Karamar Hukumar Ringim.
Jami’in hulda da Jama’a na rundunar ‘yan sandan ta Jiha ASP Lawan Shiisu shine ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse.
A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis lokacin da ’yan sanda daga kananan hakumomin Jahun, da Ringim, da kuma ’yan banga a lokacin da suke sintiri, inda suka hango yan bindigar akan babura akan hanyar Jahun zuwa Ringim inda suka bi sawun.
ASP Lawan Shiisu Adam, ya ce a lokacin da yan bindigar suka gano cewa yan sanda sun tare hanyar, shine suka shiga cikin Daji.
Haka kuma ya ce duk da cewa wadanda ake zargin sun tsere, sai da rundunar hadin gwiwar ‘yan sintiri ta dauki matakin tsaurara Sintiri a Dajin.