Ribadu ya musanta rade-radin cewa yana shirin tsayawa takarar shugaban kasa

Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Mallam Nuhu Ribadu, ya musanta rade-radin cewa yana shirin tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2031, yana mai cewa ya mayar da dukkan hankalinsa kan nasarar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne kawai.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Ribadu ya yi watsi da zarge-zargen tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya ce yana hada kai da Gwamna Uba Sani na Kaduna da Hukumar ICPC domin bata masa suna.

El-Rufai ya yi wannan zargi ne yayin wata hira da aka yi da shi a Arise TV, inda ya ce Ribadu na kulla makarkashiya don cimma burinsa na siyasa.

Sai dai a martaninsa, Ribadu ya jaddada cewa ba shi da sha’awar duk wata hayaniya ta siyasa, yana mai cewa ya fi karkata ga aiwatar da nauyin da aka dora masa a matakin kasa.

Comments (0)
Add Comment