Gwamnatin Jihar Kano ta dora Alhakin sauyin yanayi da ambaliyar ruwa kan rashin tsaftar muhalli da kuma zuba shara akan hanyoyi da magudanan ruwa da ke sassan Jihar.
Gwamnatin Jihar ta ce ta’adar sare bishiyoyi a dazuka da kuma birane ba tare da dasa wasu ba, na daga cikin abubuwan da suke haifar da matsalar sauyin yanayi ga kasa.
Kwamishinan Muhalli na Jihar Kano, Dr Kabiru Ibrahim Getso, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan nasarorin da hukumar ta samu cikin shekarar 2022.
Dr Kabiru Getso, ya ce akwai bukatar a hada hannu wuri guda domin magance matsalar sauyin yanayi wanda yanzu haka ya zama babbar barazana ga Duniya, inda ya kara da cewa Talakawa suna da rawar da zasu iya takawa domin tunkarar matsalar.
Kazalika, ya bukaci mutanen Jihar su daina zuba shara a wuraren da bai kamata ba, tare da rike ta’adar dashen bishiyoyi a muhallan da ake rayuwa.