Rashin daidaito a nade-naden mukamai na kawo cikas ga hadin kan Nijeriya – Sanata Ndume

Rashin daidaito a nade-naden mukamai na kawo cikas ga hadin kan Nijeriya – Sanata Ndume

Sanata Mohammed Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, ya nuna damuwarsa kan yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke raba mukaman gwamnati, yana mai zargin cewa ana nuna fifiko ga wasu yankuna bisa tsarin da bai dace ba.

A wata hira da Arise TV, Ndume ya ce nade-naden sun saba da tsarin tarayya da dokar kasa, yana mai kira ga shugaban kasa da ya sake duba lamarin don tabbatar da adalci.

Ya ce matsayin sa na dan majalisa yana bashi damar yin magana idan ya ga kuskure, musamman idan hakan na iya barazana ga hadin kai da zaman lafiya a Nijeriya.

Comments (0)
Add Comment