Kimanin gidaje 40 ne Gwamnatin jihar Nassarawa tace ta rushe, wadanda aka gina ba bisa ka’ida ba a hanyoyin ruwa, cikin kananan hukumomi 3 jihar.
Haka kuma tace an kama mutane 27, tare da gurfanar dasu a kotun tafi da gidanka, bisa take dokar tsaftar muhalli ta wata wata, da ake wanzarwa a jihar.
A wani labari kuma wata ambaliyar ruwa tayi sanadiyar rushewar kimanin shaguna 6, hadi da wasu gidaje, biyo bayan saukar ruwan sama a jihar.
- Hisba ta kai samame wasu gidajen sayar da barasa uku a jihar Jigawa
- Aƙalla mutane uku ne suka rasu a wani sabon rikicin manoma da makiyaya a Jihar Nasarawa
- Jam’iyyar PDP ta sanar da ɗage babban taron shugabaninta na ƙasa
- Ƙungiyar Tuntuɓa ta Dattawan Arewa ta dakatar da shugaban majalisar ƙolinta
- Za’a dauki matakin kafa ‘yan sandan jihohi a Najeriya
- Obasanjo ba shugaban da za a yi koyi da shi bane – Gwamnatin Tarayya
Babban jami’in kula da muhali na ma’aikatar muhalli da albarkatun kasa, Mallam Abubakar Mohammad, shine ya sanar da hakan gay an Jaridu, yayin ziyarar gani da ido, kan yadda shirin tsaftar muhalli ta wata wata ke gudana a Lafia, babban birnin jihar.
Yace gwamnati na daukar matakan ne a kokarin kawo karshen matsalar ambaliyar ruwa a jihar.
Haka kuma yace dabi’ar kunnen kashi da wadansu mutane keyi ga umarnin gwamnati, kan hani da yin gine gine a hanyoyin ruwa, itace ta sanya aka dauki matakin yin rusau.