Rasha ta bayyana jin daɗinta kan cacar-bakin shugabannin Trump da Ukraine

Rasha ta bayyana jin daɗinta kan cacar-bakin da aka yi tsakanin shugaban Amurka da shugaban Ukraine a fadar gwamnatin Amurka.

A jiya Juma’a ne cacar-baki ta kaure a tsakanin shugabannin biyu bayan Shugaban Ukraine Zelensky ya je ofishin shugaban Amurka domin tattaunawa yiwuwar tsagaita wuta a yaƙin ƙasarsa da Rasha.

Trump ya shaida wa Zelensky cewa ya cimma yarjejeniya da Rasha ko “mu rabu da kai”.

Tsohuwar mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakhrova ta ce shugaba Trump ya nuna dattako da bai kai wa mista Zelensky bugu ba.

A nasa ɓangaren, kwamandan sojojin Ukraine ya ce dakarunsa suna goyon bayan duk wani mataki da Zelensky ya ɗauka.

Sai dai su kuma ƴan Jam’iyar Hamayya ta Democrat a Amurka sun ce Trump ya zubar da ƙimar ƙasar a idon duniya.

Comments (0)
Add Comment