Oluremi Tinubu ta yi kira ga ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri

Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu ta yi kira ga ƴan kasar da su ƙara haƙuri, inda ta ce lallai akwai haske a gaba.

Oluremi ta bayyana haka ne a saƙonta na Kirsimeti ga ƴan kasar, inda ta ƙara da godiya bisa haƙuri da goyon bayan da suke bayarwa wajen gina kasar. A cewartsa, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a shirye yake ya kawo gyare-gyare da za su inganta rayuwar ƴan kasar, waɗanda tuni wasu daga ciki sun fara nuna alamar nasara.

Comments (0)
Add Comment