Ofishin kula da basussuka na kasa yace ana bin Najeriya bashin kudi Naira Tiriliyan 25 da Biliyan 700

Ofishin kula da basussuka na kasa yace jumillar bashin da ake bin Najeriya ya kai kudi Naira Tiriliyan 25 da Biliyan 700.

Darakta-Janar ta ofishin, Miss Patience Oniha, ita ta bayyana haka yayinda take jawabi ga kwamitin kula da asusun kudaden gwamnati na majalisar wakilai ta kasa a Abuja.

Patience Oniha tace basussukan da aka ciwo daga kasashen ketare sun kai kashi 32 cikin 100 na jumillar bashin, yayinda kashi 68 cikin 100 na cikin gida ne.

Tayi bayanin cewa ofishin na kula da basussuka na kasa, hukuma ce ta gwamnati wacce ta fara aiki a shekarar 2000 biyo bayan matsalolin basussukan da kasar ke fuskanta wanda ya jawo yafe bashin da aka yi a wancan lokacin.

Patience Oniha tace alhakin hukumar ne kula da basussukan gwamnati, kuma daga cikin aikinta akwai ciwo bashi a madadin gwamnatin tarayya.

Comments (0)
Add Comment