Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP Peter Obi ya mayar da martani kan wata murya da ke yawo a shafukan sada zumunta.
Ana zargin cewa muryar na wata tattaunawa ce ta waya tsakanin Obi da shugaban cocin Living Faith, Bishop Oyedepo.
Hakan na zuwa ne bayan kimanin kwana biyar da ɓullar muryar.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na tuwita a jiya Laraba, Obi ya ce ce-ce-ku-cen da ake yi kan muryar wata maƙarkashiya ce da jam’iyya mai mulkin ke yi na tursasa masa ya bar Najeriya.
Peter Obi dai ya nesanta kansa da muryar da ake ta yaɗawa a shafukan sada zumunta da kuma jaridun ƙasar.
Muryar dai ta haifar da zazzafar muhawara saboda irin kalaman da ɗan takarar shugaban ƙasar ya yi a cikin wayar, waɗanda ake ganin ba su dace da shi ba.