Obasanjo Ya Roki Kotun Birtaniya Ta Sassauta Wa Ekweremadu

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya rubuta wa jami’an kotu a Birtaniya , inda yake bukatar a yi sassauci lokacin yanke wa sanatan Najeriya Ike Ekweremadu da matarsa hukunci bayan kama su da laifin ‘safarar sassan jikin ɗan bil’adama.’
A watan da ya gabata ne kotu ta samu sanata Ike Ekweremadu mai shekara 60 da matarsa Beatrice da kuma wani likita Dr Obinna Obeta da laifin ɗaukar wani matashi ɗan shekara 21 daga Legas zuwa Birtaniya domin cire ƙodarsa, domin a bai wa ƴarsa Ekweremadu, mai suna Sonia, mai shekara 25.
A wasikar da Obasanjo ya rubuta, ya ce abin da ma’auratan suka yi ba daidai ba ne kuma babu wata al’umma da za ta lamunci aikata hakan.
Sai dai ya bukaci kotun da ta duba lamarin ƴar sanatan wadda lafiyarta ke cikin haɗari da kuma ke son agajin lafiya na gaggawa domin sassauta masa.
Obasanjo ya kuma faɗa wa kotun cewa ta duba ɗabi’u masu kyau da Ekweremadu ke da su a lokacin yanke masa hukunci.
Sai dai babu tabbacin cewa ko wasikar da Obasanjo ya rubuta za ta iya yin tasiri.
Tsohon shugaban ƙasar dai bai bayyana cewa ko yana magana da yawun gwamnatin Najeriya ba ne.
Sanata Ekweremadu da matarsa na tsare a hannun jami’an Birtaniya har zuwa 5 ga watan Mayu lokacin da za a yanke masa hukunci, karo na farko da ake yanke wa wani hukunci karkashin hana bauta ta zamani.

Comments (0)
Add Comment