Obasanjo ya nemi shugabanni suyi amfani da tarin albarkatu da Najeriya ke dashi domin ciyar da ita gaba

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayi kira ga shugabannin kasar nan da suyi amfani da tarin albarkatu da kasar ke dashi domin ciyar da ita gaba, yana mai cewa Ubangiji bai halicci Najeriya domin tasha wahala ba, domin ya azurta ta da abinda bai azurta sauran kasashen duniya ba.

Ya bayyana haka ne a wani taron addini daya halarya a Abuja karo 40 a jiya Lahdi, yana mai jaddada cewa Najeriya tana da dukkan abinda take bukata domin ta wanzu cikin arziki.

Obasanjo ya bukaci shugabanni, malamai da sauran yan kasa su dukufa wajen yiwa kasa addu’a kan halin da ta fada, yana mai cewa halin da ta shiga ba laifin ubangiji bane. Shugaban kasa Bola Tinubu wanda ya samu wakilcin ministan Abuja Nyesom Wike ya godewa cocin bisa kokarin ta na samar da daidaiton zamantakewa, ilimi da samar da tallafin jin kai.

Comments (0)
Add Comment