Nuhu Ribadu ya kira wani taro na sirri da kungiyar gwamnonin Arewa da shugabannin tsaro

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, ya kira wani taro na sirri da kungiyar gwamnonin Arewa da shugabannin tsaro da suka hada da Sufeto Janar na ‘yan sanda da kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya akan yaki da matsalar satar mutane kasar nan.

Taron wanda ya gudana a jiya Alhamis a Abuja, ya dauki sama da sa’o’i hudu, kuma bayan taron, shugaban kungiyar Gwamnoni Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya bayyana sakamakon taron.

Ya sanar da shirin da kungiyar zata yi na duba wasu hanyoyin da za a bi domin kawo karshen matsalar rashin tsaro da ke kara kamari a arewacin kasar nan.

Gwamnan ya kara da cewa, za a tallafa wa sojoji hanyoyi da dama  don dakile tashe-tashen hankula. A makon da ya gabata ne wasu ‘yan bindiga suka sace dalibai kusan 300 a wata makaranta a garin Kuriga da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Comments (0)
Add Comment