Tsohon Gwamnan jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce jam’iyyarsa ce za ta doke manyan jam’iyyun APC da PDP domin samun nasara a zaɓen 2027.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wurin babban taron jam’iyyar NNPP a Abuja a ranar Alhamis, inda ya ce ƴan Najeriya ba sa jin daɗin yadda gwamnati take gudana a yanzu.
“Na yi amannar cewa idan za a yi zaɓe sahihi a ƙasar nan, jam’iyyarmu ce za ta samu nasara, domin za ta kayar da APC da PDP da duk sauran jam’iyyun ƙasar nan,” in ji shi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A game da batun cewa NNPP ta dare gida rabu, Kwankwaso ya ce babu wani rikici a jam’iyyar, inda ya ce “bai kamata a yi maganar ba ma, domin na san akwai masu samun abinci a sanadiyar wannan saɓani. Amma su sun san wasa suke yi.”
Kwankwaso ya yaba wa ƴan Najeriya bisa ƙaunar da suka nuna masa ba, inda ya ce, “ƴan Najeriya ba sa jin daɗi. Akwai talauci a ƙasar, akwai matsalar tsaro, sannan ababen more rayuwa sun taɓarɓarewa, kuma ba ma ganin wata huɓɓasar magance su,” in ji shi.