Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Cif Timipre Sylva, a jiya, ya ce Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) yana asara wajen sayar da man fetur saboda umarnin da gwamnatin tarayya ta ba shi bisa tallafin mai.
Kalaman na Timipre Sylva na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan kasuwar mai suka bayyana cewa, matsalar samar da mai da ke haifar da karancin mai, na iya ci gaba har zuwa watan Yuni, bisa shirin gwamnati na kawo karshen tallafin man fetur a watan Yuni.
Ministan man na fetur ya yi magana ne a Abuja yayin da aka dawo shirin shelar nasarorin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Timipre Sylva, yayin da yake magana a Abuja jiya ya dage cewa tallafin ya kasance nauyi amma ya jaddada cewa nauyi ne a wuyan NNPC wanda ya sanya kamfanin mai ya ci gaba da tafka asara yayin sayar da man fetur.
A makon jiya ne Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-tsare ta Kasa, Zainab Ahmed, ta ce Gwamnatin Tarayya ta ware kudi kimanin Naira Tiriliyan 3 da miliyan dubu 600 domin tallafin man fetur har zuwa watan Yunin 2023.