NNPC ta fitar da kiyasin farashin man fetur da aka samu daga matatar man Dangote

Da sanyin safiyar yau ne hukumar NNPC ta fitar da kiyasin farashin man fetur da aka samu daga matatar man Dangote a gidajen sayar da man da ke fadin kasar nan, inda ta jaddada cewa bisa tanadin dokar masana’antar man fetur (PIA), ba gwamnati ce zata kayyade farashin man fetur ba. 

A cikin takardar da aka makala, hukumar NNPC ya bayyana cewa man da ake samu daga matatar Dangote za a sayar da shi kan Naira 950.22 kan kowace lita a Legas; N960.22 a Oyo; N980.22 a Rivers; N992.22 a Abuja; N999.22 a Kaduna; N999.22 a Kano; N999.22 a Sokoto da kuma N1,019 a Borno, bisa tsarin farashi na watan Satumba.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar NNPC ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa matsalar karancin man fetur da kuma dogayen layukan da ake fama da su a gidajen man za su bace nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.

Kamfanin mai na kasa ya kuma jaddada cewa, ba za a kayyade farashin man fetur daga matatar man fetur din NNPC ko Dangote ba, yana mai cewa daga yanzu yan  kasuwa ne za su kayyade farashin man fetur.

Comments (0)
Add Comment