Nima na amfana da filayen da gwamnatin Ganduje ta raba – Muhuyi Magaji

Awani cigaban kuma Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Rimingado, ya amince da cewa shi ma ya amfana da daya daga cikin filayen da tsohuar gwamantin Ganduje ta sayar ba bisa ka’ida ba, wadanda yanzu haka akayiwa alamar ruguje wa.

Ya yarda cewa tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ne ya ware masa daya daga cikin filayen amma daga baya ya sayar da shi.

Rimingado, wanda kuma mamba ne a kwamitin da Gwamna Abba Yusuf ya kafa domin ruguza gine ginen da akayi ba bisa ka’ida ba, ya tabbatar wa Sawaba cewa an ware masa wani fili ne a kewayen yankin da akayi alamar rugujewa.

Kafin hakan dai a makon da ya gabata ne gwamnatin jihar ta yiwa wasu kadarori alamu domin rugujewa, ciki har da wanda Ganduje ya baiwa Rimingado.

Daga cikinsu akwai filayen wasa da gidajen mai da ke kan titin BUK da kuma kadarori da aka gina a katangar birnin Kano da aka rushe.

Comments (0)
Add Comment