Nigeria Ta Samu Tallafin $800M Gabanin Cire Tallafin Man Fetur

Gwamnatin tarayya ta samu tallafin dala miliyan 800 daga Bankin Duniya domin bunkasa shirinta na inganta rayuwar al’umma gabanin cire tallafin man fetur a watan Yunin wannan shekara, daidai lokacin da tattalin arzikin ƙasar ke tafiyar hawainiya.
Ministan kasafin kudi da tsare-tsare Zainab Ahmad ce ta sanar da haka ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan zaman Majalisar zartarwa yau a Abuja.
Gwamnati ta ce za a raba tallafin ne ta hanyar amfani da na’urar aika kuɗi ga ‘yan Najeriya kusan miliyan 50 ko gidaje miliyan 10, inda ta ce waɗannan mutane suna cikin mafi raunin rukunin al’umma.
Ta ce hakan na da nufin rage tasirin cire tallafin man fetur kan al’umma.
Bankin Duniya ya damu a kan cewa ƙaruwar tattalin arzikin da Najeriya ta samu na kashi 2.8, bai wadatar ba wajen rage tasirin fiye da kashi 40 na al’ummar da ke fama da matsanancin talauci.
Najeriya da ta kasance ƙasa mafi girman tattalin arzikin a Afirka, ta ware naira tiriliyan 3.36 a bana domin kashewa a matsayin tallafin man fetur har zuwa tsakiyar shekara ta 2023 lokacin da za ta daina biya.
Najeriya ita ce ƙasa mafi yawan arzikin danyen mai a Afirka amma tana shigo da man fetur daga ƙasashen waje saboda rashin aiki da matatunta na mai ke yi.

Comments (0)
Add Comment