NDLEA ta kama wasu masu safarar miyagun kwayoyi guda 422 a jihar Jigawa

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Jigawa ta kama wasu masu safarar miyagun kwayoyi guda 422 tare da kwace miyagun kwayoyi da nauyinsu ya kai kilogiram 999.335 da sauran kayan maye.

Kwamandan Hukumar NDLEA ta Jihar Mu’azu Aliyu Dan Musa ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a lokacin da yake zantawa da manema labarai a wajen taron tunawa da ranar yaki da shan miyagun kwayoyi da safarar miyagun kwayoyi ta duniya da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.

Ya ce daga watan Yunin bara zuwa watan Yunin da muke ciki rundunar ‘yan sandan ta yi nasarar kame masu safarar miyagun kwayoyi guda 422.

Ya kuma ce daga cikin adadin 409 maza ne da mata 13.

Ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma, shugabannin gargajiya da na addini, da shugabannin kananan hukumomi da su hada kai da rundunar domin tabbatar da yaki da ta’ammali da muggan kwayoyi.

Comments (0)
Add Comment