Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun cafke wani dillalin kayayyakin gyaran mota da ke zaune a Legas, Levi Ubodoeze, bisa yunkurin safarar hodar iblis mai nauyin kilo biyu da aka boye a cikin injinan motoci zuwa kasar Angola.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya sanar da kamen a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi.
Ya ce an kama mutanen ne ta hanyar musayar bayanan sirri da hadin gwiwa tsakanin NDLEA da hukumomin Angola.
Haka kuma hukumar ta gano wani adadi mai yawa na sinadarin phenacetin, mai nauyin kilogiram 75.50, wanda aka yi masa lakabi da Semolina.
A cewar sanarwar, Ubodoeze ya amince cewa yana da hannu a cinikin hodar ibilis a lokacin da yake siyar da kayayyakin gyaran motoci a Kasuwar Ladipo, Mushin, Legas.
Ya kara da cewa, a wani samame da jami’an NDLEA suka yi, sun kama wata motar kasuwanci a unguwar Ojo da ke jihar Legas a ranar 7 ga watan Maris, inda suka kama wasu mutane biyu, China Michael da Igbo Ekene.