Nan gaba kada Najeriya zata samu ababan hawa masu amfani da hasken rana

Gwamnatin tarayya tace nan gaba kada Najeriya zata samu ababan hawa masu amfani da hasken rana mafi girma a Nahiyar Afrika.

Da yake jawabi a taron koli kan sauyin yanayi na majalisar dinkin Duniya, Ministan harkokin kasashen Yusuf Tuggar, ya bayyana bukatar da ke akwai na maida hankali domin magance matsalar sauyin yanayi da duniya ke fuskanta.

Yusuf Tuggar yace Najeriya na da niyyar mallakar ababan hawa masu amfani da wutar lantarki mafi girma a Afrika,inda aka kara adadin motoci masu amfani da wutar lantarki daga 100 zuwa 1,000.

Ya kara da cewa kasar nan na jagorantar yaki da matsalar sauyin yanayi a Afrika ta hanyar samar da manufofi masu kyau.

Ministan yayi kira ga shugabannin duniya su kauda bambancin siyasa a hada kai wuri guda domin samar da manufa mai ma’ana a yaki sauyin yanayi. Yana mai cewa akwai bukatar kasashe masu karfi su tallafawa kasashen dake tasowa ta fannin tattalin arziki.

Comments (0)
Add Comment