Najeriya ta tabbatar da rasuwar Alhazanta 15 daga cikin Alhazan da suka yi aikin hajji bana

Najeriya ta tabbatar da rasuwar alhazanta 15 daga cikin alhazan nata fiye da dubu 50 da suka yi aikin hajjin bana da aka kammala a Saudiyya.

Hukumar Alhazan ƙasar ce ta tabbatar da hakan a yayin taron manema labarai da ta gudanar na bayan kammala Arfa, a Makkah.

A ranar Laraba ne aka kammala aikin Hajjin na bana a hukumance, wanda ya ƙare cikin alhini sakamakon mutuwar ɗaruruwan alhazai.

Saudiyya ba ta bayyana adadin alhazan da suka mutu ba a hukumance, kodayake hukumomi sun ce an kai rahoton sama da mutum 2,700 da suka yi fama da bugun zafi a ranar Lahadi kaɗai. Sai dai a cewar kamfanin labarai na AFP bayan tattara bayanai daga ofisoshin jakadancin ƙasashe, aƙalla alhazai 922 ne suka mutu yayin aikin Hajjin akasari saboda tsananin zafi da aka yi fama da shi

Comments (0)
Add Comment