Najeriya ta samar da jiragen yaki marasa matuki da bama-bamai a karon farko

Rundunar sojin Najeriya tare da kamfanin fasaha na Briech UAS sun gabatar da jiragen yaki marasa matuki da bama-bamai na farko da Najeriya ta samar.

A wajen bikin gabatar da wadannan makamai a Abuja, Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce hakan wata babbar nasara ce ga Najeriya wajen zama mai dogaro da kanta a fannin tsaron kasa.

Ya bayyana cewa wadannan jiragen marasa matuki za su taimaka wajen tattara bayanan sirri da kuma yaki da ‘yan ta’adda, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar matsalolin tsaro masu sarkakiya.

A nasa bangare, Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya ce wadannan makamai za su taka muhimmiyar rawa wajen kare iyakokin kasa, yana mai cewa jihohi kamar Filato sun riga sun fara amfani da wasu daga cikin wadannan fasahohi don yaki da ‘yan ta’adda.

Comments (0)
Add Comment