Najeriya ta fara gwajin cutar HMPV kan fasinjojin da ke shiga ƙasar

Gwamnatin Najeriya ta ƙara ƙaimi wajen sa ido a manyan filayen jiragen ƙasar domin hana yaɗuwar cutar HMPV da ta ɓulla a ƙasar China a ƙasar.

Daily Trust ta ruwaito cewa ministan lafiya na ƙasar, Muhammad Ali Pate, ya umarci ma’aikatan lafiya da ke filayen jirage su fara gwada fasinjojin da ke shiga ƙasar domin gano suna ɗauke da cutar, inda jaridar ta ce an fara gwajin ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas da na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

A lokacin da cutar Covid-19 ta ɓulla a shekarar 2020, wani fasinja mai shekara 44 ɗan asalin ƙasar Italiya ne ya shigar da cutar Najeriya ta filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a ranar 24 ga Fabrairun 2020.

Cutar ta HMPV, wadda ta fara ɓulla a China, yanzu ta fara yaɗuwa a India da Malaysia da Kazakhstan, sannan aƙalla mutum 5,000 ne ake tunanin cutar ta kwantar a Birtaniya.

Comments (0)
Add Comment