Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bukaci taimakon gwamnatin Amurka, domin magance matsalar tsaro a Najeriya.
Babban mai taimakawa kan harkokin yada labarai da sadarwa na ofishin mataimakin shugaban kasa Stanley Nkwocha ya bayyana haka a wata sanarwa daya fitar jiya a Abuja.
Stanley Nkwocha yace Kashim Shettima yayi rokon lokacin da ya hadu da shugaban tawagar bunkasa samar da abinci ta Amurka Cary Fowler a wani bangare na ziyarar aiki daya ke gabatarwa a Amurka.
Mataimakin shugaban kasa ya kuma bayyana wasu bangarori masu muhimmanci da Najeriya ke bukatar tallafin Amurka da suka hada fannin aikin gona. Shattima ya tabbatarwa tawagar shirin Najeriya da gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu domin yin hadin guiwa wajen bunkasa aikin gona a nahiyar Afrika.