Najeriya ta bayar da lasisin gina sabbin matatun man fetur uku

Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, NMDPRA, ta bayar da lasisin kafa sabbin matatun man fetur uku a wasu jihohin ƙasar uku.

Cikin wata sanarwa hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta bayar da lasisin gina sabbin matatun ne a jihohin Abia da Delta da kuma jihar Edo.

NMDPRA ta ce sabbin matatun uku idan an kammala su za su iya tace gangan 140,000 a kowace rana.

Bayanai daga hukumar ta NMDPRA sun nuna cewa Najeriya na da matatun man fetur tara, ciki har da sabuwar matatar Dangote da ke birnin Legas.

Waɗannan matatu na tace ganga 974,500 a kowace rana, yayin da matatar Dangote kaɗai ke da ƙarfin tace ganga 650,000 a kowace rana.

– BBC Hausa

Comments (0)
Add Comment