Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, ya ce Najeriya ba ta samun sahihan alkaluman adadin kuri’un gaskiya da ake kadawa a yayin zabe, saboda shigar masu zaben boge cikin tsarin zabe.
Ya bayyana cewa mafi alheri ga shugaban INEC da jami’ansa su yi murabus idan ana matsa musu lamba su tafka magudi maimakon su amince da hakan.
Jonathan ya yi wannan jawabi ne a taron kungiyar YIAGA Africa kan zabe a yammacin Afirka da aka gudanar a Abuja.
Ya ce har sai an samu mutane masu rikon amana a INEC da za su fi son yin murabus maimakon su lalata zabe, to sai nan gaba ne tsarin zabe zai samu cikakken inganci.
Jonathan ya bukaci a yi gyara a tsarin domin tabbatar da sahihin zabe da nagartattun shugabanni.