Najeriya ba ta kaimatakin da za’a kirkiri ‘yan sandan jihohi ba – Kayode Egbetokun

Sufeto Janar na ‘yan sandan kasa, Kayode Egbetokun, ya yi imanin cewa kasar nan ba ta kaimatakin da za’a kirkiri ‘yan sandan jihohi ba duk da dimbin kalubalen tsaro da ake fuskanta.

Ya yi wannan jawabi ne a safiyar yau yayin wata tattaunawa ta kasa kan ‘yan sandan jihohi da aka gudanar a Abuja mai taken Hanyoyi zuwa Zaman Lafiya: sake fasalin aikin yan sanda a Najeriya.

Babban sufetan ya ce gwamnonin jihohi na iya amfani da jami’an ‘yan sandan da ke karkashinsu domin cimma wata manufa ta siyasa ko ta kashin kai da kuma tauye hakki da tsaro.

Ya kuma ba da shawarar wasu abubuwa da za su sa ‘yan sanda su kara inganta tsaron kasar.

A cewar shugaban ‘yan sandan, akwai kuma bukatar a kara daukar ma’aikata aiki duk shekara, bayar da karin horo ga jami’an ‘yan sanda da sauran su, na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da tsaron Najeriya. Taron wanda ya samu halartar manyan kusoshi da dama a kasa, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya yi imanin cewa duk da kalubalen da ake fuskanta, ‘yan sandan jihohi bazasu zama mafita ga kalubalen tsaron kasa ba.

Comments (0)
Add Comment