NAFDAC ta ce ta karbe wasu magungunan da USAID take bayarwa a matsayin tallafi

Hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta ce ta karbe wasu manyan motoci na kayan magani da take zargi sun daina aiki, hadi da magungunan da USAID take bayarwa a matsayin tallafi, da dai sauransu.

Darakta Janar na Hukumar ta NAFDAC farfesa Mojisola Adeyeye, shine ya ya bayyana hakan a jiya laraba.

Hukumar ta NAFDAC dai yanzu haka tana ci gaba da gudanarda ayukkan ta na kakkabe miyagun kwayoyi a fadin tarayyar najeriya musamman yada take fadada samamen ta a manyan kasuwannin sayarda magunguna dake kasar nan.

Comments (0)
Add Comment