Mutum 27 ne suka mutu yayin da wasu kwale-kwalen ‘yan cirani suka nutse a gaɓar tekun Tunisia.
Kwale-kwalen farko ya bar Tunisia ne a ranar Juma’a inda ya nufi Italiya ɗauke da mutum 37.
Mutum 20 sun bata yayin da aka ceto wasu 17 na daban, in ji kakakin kotun birnin Sfax.
A ranar Asabar, an gano gawarwaki huɗu a bakin ruwa bayan kwale-kwale na biyu ya nutse.
An ceto mutum 36 a kwale-kwale na biyu, a cewar kakakin mutum uku na daban sun ɓata.
Kakakin Faouz Masmoudi ya ce duka kwalekwalen na roba ne.
Tun farkon watan Maris an samu nutsewar jiragen ‘yan cirani bakwai a wannan gaɓar kogin.
Wata gaɓar tekun a Tunisia ba ta fi nisan kilomita 150 zuwa Lampedus ba, wani tsuburi a Italiy, wanda duk wanda ya isa nan ana masa kallon yana cikin Italiya.