Mutum 16 sun rasu sanadiyyar haɗarin babbar mota a jihar Kano

Wani hatsarin babbar mota da ya auku a birnin Kano ya yi ajalin mutum 16.

Cikin wata sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kiyaye aukuwar hadurra ta jihar Kano, Abdullahi Labaran ya fitar, ya ce hatsarin ya auku ne ranar Alhamis da daddare a kan babbar gadar Muhammadu Buhari da ke unguwar Hotoro.

Abdullahi Labaran ya ce lamarin ya faru sakamakon gudu da direban motar ke yi, lamarin da ya sa ta ƙwace masa a daidai gadar.

Ya ƙara da cewa hatsarin ya rutsa da mutum 71 da motar ke ɗauke da su yayin da mutum 52 suka samu raunuka, mutum 16 kuma suka mutu.

Tuni aka kai waɗanda suka jikkata asibin Murtala da ke birnin na Kano domin ba su kulawar da ta dace.

Hatsarin manyan motoci a kan titunan ƙasar na ƙara haifar da fargaba, inda a lokuta da dama idan motocin suka faɗi ake rasa rayuka da asarar dukiyoyi.

Ko a farkon makon nan ma wata babbar mota ɗauke da dabbobi da faɗi a jihar Neja, da ke arewa ta tsakiyar ƙasar.

Comments (0)
Add Comment