Mutane 40 sun Rasu sanadin ambaliya a Jigawa, ana cigaba da nema

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar jigawa ta tabbatar da mutuwar akalla mutane 40 a fadin jiharnan inda tace dubbun mutane ne suka tserewa muhallinsu da asarar gonakinsu sanadiyyar iftila’in amballiyar ruwa.

Shugaban hukumar Sani Ya’u Babura wanda ya tabbatar da mutuwar mutanen, yace hukumar su ta kammala tattara duk wani bayanai da zata turawa jami’anta domin bayar da agajin gaggawa ga wadanda iftala’in ya afkawa.

Sani Babura ya kara da cewa sunyi kokari sosai wajan tattara adadin mutanen da suka rasa rayukansu, gonakinsu da wadanda suka tserewa muhallinsu.

Mutane na hijira saboda ambaliya

Ya kara da cewa baya ga haka, Gwamnatin jihar jigawa na bukatar taimakon hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA.

Flood
Comments (0)
Add Comment