Mutane 25 sun mutu sakamakon jirgin ruwa da ya nutse a yankin Gbajibo

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane 25 bayan da wani jirgin ruwa ya nutse a yankin Gbajibo da ke Karamar Hukumar Mokwa.

A ranar 1 ga watan Oktoba, wani jirgin ruwa mai dauke da sama da fasinjoji 200 da ya taso daga Gbajibo da nufin zuwa wajen Maulidi ya kife.

Darakta Janar na hukumar NSEMA, Abdullahi Baba-Arah, ya ce hukumar ta fara gano gawar mutane tara ne, sannan ta sake gano wasu gawarwakin wasu mutane 16 a yayin aikin ceto da ta gudanar.

Cikin wadanda suka rasu akwai maza 21 da mata hudu.

Har yanzu ana ci gaba da neman sauran fasinjoji 125 da suka bace.

Ya kara da cewa, aikin ceto na ci gaba da gudana, yayin da jihar ke jimamin mutuwar wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan hatsari.

Comments (0)
Add Comment