Mun gani kuma mun yaba, a cewar Sarkin Kano ga Gwamna Badaru

Sarkin Kano, Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yabawa gwamna Muhammadu Badaru Abubakar bisa aiwatar da ayyukan raya kasa a jihar Jigawa.

Ya sanar da haka lokacin da ya kaiwa gwamnan ziyara a gidan gwamnatin dake Dutse.

Sarkin ya bayyana cewa yayin ziyararsa zuwa masarautun jiharnan, ya yaba da ayyukan da suka kawata birane da yankunan karkara a fadin jihar.

Aminu Ado Bayero ya gayawa gwamnan cewa yazo jihar ne domin gabatar da kansa tare da neman shawarwarin sarakunan, inda ya godewa mutanen jiharnan bisa kyakykyawar tarbar da suka yi masa.

Da yake mayar da martani, Gwamna Badaru Abubakar yace yayi farinciki da alfahari da ziyarar sarkin, wacce yace zata karfafa danganta mai kyau da tarihi tsakanin mutanen jihoshin Kano da Jigawa.

BadaruJigawasarkin Kao
Comments (0)
Add Comment