Mummunan yanayi da rashin kyawawan hanyoyi a Japan ya kawo tsaikon aikin masu ceto a jiya juma’a da ake cigaba da neman mutane 222 da suka bace kwanaki 4 bayan gagarumar girgizar kasa ta hallaka sama da mutane 100.
An kubutar da wasu dattijan mata 2 a ranar alhamis, amma masu ceton na da burin gano karin wasu bayan girgizar kasar mai karfin maki 7.5 a yayin murnar sabuwar shakera bayan mamakon ruwan sama, da Kankara a cikin kwanakin nan.
Dubban masu aikin ceton a dukkan fadin kasar ta Japan na cigaba da fama da munanan hanyoyi sakamakon zaftarewar kasa da zaizaya a yankin Ishikawa domin isa ga daruruwan kauyuka da suka tagayyara.
Sa’o’I 72 bayan girgizar kasar, anyi nasar ceto matan masu shekaru a raye daga baraguzan gine-ginen su a yankin Wajima. Akalla iyalai dubu 30 ne ke rayuwa ba tare da lantarki a yankin na Ishikawa mai gidaje sama da dubu 89, 900 da kuma garuruwa biyu masu makwabtaka dake cikin kishirwa.