Ministar mata ta ce za ta sasanta rikicin dakatar da Sanata Natasha

Ministar al’amuran mata da walwalar jama’a ta Najeriya, Imaan Suleiman ta ce a shirye take ta shiga domin sasanta rikicin dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta tsakiya.

Yayin da take jawabi ga manema labarai a fadar shugaban ƙasar ranar Juma’a, ministar ta bayyana takaicinta kan zargin cin zarafin lalatar da aka yi a majalisar dattawan, lamarin da ta bayyana da ”abin takaici”.

Tana mai cewa bai kamata irin wannan abu ya riƙa faruwa a majalisar dokokin Najeriya ba.

Imaan Sulaiman ta ce ma’aikatarta za ta tattauna da majalisar dattawan domin duba yadda za a sasanta matsalar cikin salama.

“Za mu sasanta batun. Za mu tattauna da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da sasanci cikin kwanciyar hankali.”

A ranar Alhamis ne Majalisar Dattawan Najeriya ta dakatar ta dakatar da Sanata Natasha na tsawon wata shida, saboda saɓanin da ya shiga tsakaninta da shugaban majalisar, kan sauya mata wurin zama, inda daga baya ya koma zargin cin zarafin lalata.

Comments (0)
Add Comment